|
‘Kabilar
hausawa kamar kowacce ‘kabila a duniya, tana da shahararrun
mawaka da kuma kayan kade-kade da bushe-bushe iri daban-daban.
A wannan shafi muke kawo muku wakokin kasar Hausa.
Mawakan hausawa
ba a bar su baya ba, a fannin wakoki, suna daya daga cikin
al'umman da Allah ya yiwa basira, akasarin mawakan hausawa
na rera wakoki nan take ba tare da rubutawa ba ko yin kiri'a
ba, wannan baiwa da Allah ya huwace musu ta basu damar yin
wakoki a fannonin zamantakewar rayuwar dan-adam.
Mawakan kasar
Hausa sun kasu riguni kamar haka akwai mawakan sarakuna, mawakan
manoma, mawakan 'yan dambai, mawakan kasuwa, da kuma mawakan
duk gari.
Akwai kuma salon
wakoki kamar 'yan kukuma,'yan kambara da kuma'yan garaya,
da dai sauransu. A bisa haka muke kawu muku wakokin kasar
Hausa ta na'ura mai kwakwalwa
|
|