Wannan shafi zaku iya
kama gidajen rediyo da suke watsa shirye-shiryensu a cikin harshen
Hausa. Su wadannan gidajen rediyon zaku iya jin su bisa sauti,
idan kuna da abin sarrafa sauti ta na’ura mai kwakwalwa wanda
ake kira (RealAudio), Kamar yadda aka san mu a matsayin matattarar
cibiyar binciken harshen Hausa a cikin hanyar sadarwar zamani
(internet), zamu cigaba da baku karin bayanai dangane da cigaban
Hausa a wannan duniyar tamu.
Bisa la'akari da irin
halin rayuwarmu ta yau da kullun, da kuma irin halin inda muke
zaune cikin duniya, ba duk lokaci muke dashi wanda zanu saurare
labarun duniya daga gidajen radiyo, sabo da aiyukanmu ko kuma
sabanin lokaci.
Gumel da Muryar Jama'ar
Jamus, Muryar Amurka, Muryar kasar Sin {China}, BBC London, suka
dauki nauyin kawu muku wannan labaran cikin na'urar ku mai kwakwalwa.