An haifeni a cikin garin Gumel, a ran 05
ga watan march , 1953, nayi makaranta primary a Gumel
Zango primary school, daga 1960 zuwa 1967 daga nan na
tafi babbar makarantar sakandare wadda ake kira da sunan
Kano Educational Development Center KEDC daga 1968 zuwa
1971.
Bayan gama karatu na KEDC na kama aiki da ma'aitar ilimi
ta karamar hukumar Gumel, wanda aka tura ni zuwa wani
kauye da ake kira Galadi. A wannan kauyen nayi aiki a
matsayin malamin makaranta na shekara daya. Daga nan sai
akayi min taransifa zuwa Maigatari nan ma a matsayin malamin
makaranta, nayi aikin koyarwa har zuwa lokacin da na karBa
ODOGI.
Bayan biyan kudin ODOGI na bar aikin koyarwa, na koma
aiki a ma'aikatar gona cikin 1974, wanda aka kaini Kadawa
a matsayin malamin gona wanda ake kira (Extension Walker)
inda aike noman rani. Koda yake gurin aikina yana Kadawa
amma muna zaune a cikin wani gari da ake kira Kura.
Na zauna cikin kura har tsawon shekara biyar, amma dukkan
wannan lokacin da nake zaune cikin Kura ina karatun
zama akanta ta hanyar karatun nesa ( Karatun nesa shine
wanda za su aiko maka da kayan karatu kayi da kanka).
Wannan karatun nayi da wata makaranta a London wadda
suke da jami'a a Lagos ana kiranta College of Accountancy
London. Bayan nayi karatu na kimanin wata shidda, na
kuma kasa gama wannan karatu sabo da wahalal samun aika
jarabawa da kuma samun littattafai daga makarantar.
Wannan abu yasa nabar karatun ba tare da na gama ba.
Daga nan sai na samu aiki a ma'aikatar kotunan jaha
(Judiciary Dept), a bangaren kudi a matsayin akayon
kudi. Na fara aiki cikin 1975 aikina kuwa shine shirya
takardun albashi. Na zauna a matsayin mai shirya albashi
har shekara uku, daga nan na zama mai biyan albashi
(paymaster).
Na samu zuwa karin karatu a makarantar School of Manangement
Studies Kano, wanda nayi karatun Executive Officer Accountancy,
bayan wannan karatun shine na koma babbar Ma'aikatar
kudi (Ministry of Finance) cikin 1978, amma ina aiki
a ma'aikatar alkalai.
A 1980 an mai dani Lagos Liason Office a matsayin Ma'ajin
kudi na jihar Kano, nayi aiki a Lagos har shekara uku,
daga nan an dawu dani ma'aikatar aiki watau (Ministry
of Works) a matsayin Akanta, kai na dai rike matsayi
masu dama daga mai taimakawa akanta zuwa matsayin babban
akanta.
Bayan rike wannan matsayan kuma, bisa amfani da computer
da nayi cikin aiyukana na samu matsananciyar sha'awa
ga computer. Sabo da irin wannan sha'awa tawa da computer
na nemi hanyar samun karo ilimi cikin wannan fanni.i
Alhamdu Lillahi na samu taimakon Allah da na wani dan
uwana wanda shine kwamishina a ma'aikatar kudi wanda
ake kira Mohammed Aliyu, wannan mutun ba zan manta da
shi ba a cikin rayuwa ta domin shine wanda ya bani karfin
zuciya kan wannan karatun nawa. Nayi karatun digiri
akan ilimin na'ura mai kwalkwalwa a cibiyar ilimin fasaha
ta Indiana, dake birnin Fort Wayne a Amurka. Na kuma
halarci kwasa-kwasai akan ilimin na'ura mai kwalkwalwa
a cikin Amurka.
|