Kabilar Hausa dai, kabilace dake zaune a arewa maso yammacin
taraiyyar Nijeriya da kudu maso yammacin jamhuriyyar Nijar.
Kabilace mai &imbin al'umma, kuma
a al'adance mai mutukar ha$aka, akalla
akwai sama da mutane miliyan hamsin da harshen yake asali gare
su. A tarihance kabilar Hausawa na tattare a salasalar birane.Hausawa
dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda
suka sami nasarori da dauloli kamar su daular Mali, Songhai,Borno
da kuma Fulani. A farko-farkon shekaru na 1900's, a sa'adda
kabilar Hausa ke yinkurin kawar da mulkin angizo na fulani,sai
turawan mulkin mallaka na Birtaniya suka mamaye arewancin Nijeriya,
da kuma kafa manufofin mulkin bayan gida,a bisa karkashen mulkin
birtaniya,'yan mulkin mallaka sai suka marawa fulani baya na
cigaba da manufofin angizon siyasarsu, har yanzu dai mulkin
gamin gambiza tsakanin Hausawa da Fulani shi ne yayi kane-kane
a arewacin Nijeriya.
Ko da yake, Hausawa na farko-farko maharba ne, amma da zuwan
addinin islama da kuma karbansa da hannu bibbiyu ya sanya
labari ya sha bambam.Ginshikokin al'adun hausawa na da mutukar
zaranta, <warewa da sanaiya fiye
da sauran al'ummar dake kewayenta. Sana'ar noma ita ce babbar
sana'ar hausawa, sabo da ingancin noma; hausawa ke ma sana'ar
noma kirari da cewa, na doke tsohon ciniki kowa yazo duniya
kai yatarar, akwai kuma wasu sana'o'in kamar su sha'anin jima
watau harkar fatu, rini, sa<a
da kira, fannonin dake mutukar samun cigaba a harkokin sana'o'in
hausawa. Hausawa dai sun jima da shahara wajen harkar fatauci
kana kuma masu arziki na taka rawa a sha'anin yau da kullum,
tare da masu mulki da masana. Harshen Hausa shi ne mafi girma
da kuma mafi sanai'yar harshe a nahiyar Afirka, harshen hausa
ya aro wasu kalmomi daga wasu harsuna musamman larabci kana
kuma harshen na tafiya tare da yanayin mu na zamani bisa al'adar
cu&eni-na cu&eka. Harshen
Hausa dai ya zama harshen yau da kullum ga miliyoyin jama'a
da ba hausawa bane a nahiyar Afirka.
Bugu da kari, akwai cincirindon al'ummar Hausawa a manyan
biranen yammacin Afirka da arewacinta da kuma yankunan cinikayyar
al'ummar Hausawa da kuma yankunan da Hausawa suka jima suna
bi a hanyar ta zuwa aikin hajji. Akwai kuma rubutattun adabi
masu zurfi da kasidodi da kuma rubuce-rubuce a rubutun ajami
da aka buga tun kafin zuwan turawa yan' mulkin mallaka na
birtaniyya. Har ila yau, kuma wani tsarin rubutu a ajame da
aka kirkiro tun kafin zuwan turawa, da ba kasafai ake amfani
da shi ba yanzu.
|