|
Tarishi dai yanuna cewa babu wane dalili da ke jawo yawan
'kaurace-'kaurace kamar ya'ke-ya'ke, Mutanin Gumel (Mangawa)
sunyi fama da ya'ke-ya'ken tsaron gida, tundaga inda suka
fara kaura daga Ngazargamu, yazuwa inda aka kafa garin Gumel
na yanzu. Ya'ke-ya'ke ke sawa idan jama'ar wata gundumar suka
ga alamar cewa za'a mamayesu, sai su kauracewa guri. Jama'ar
Gumel sun tabka ire-iren waddannan fa'dace-fa'dacen, da dama
kafin su kafa garin Gumel, da kuma bayan sun kafa zango a
Gumel. Gumel tana daya daga cikin garuruwan da basu nuna amincewarsu
da mulkin Hausa-Borno, ko na Sokoto ba, ko da shike Barno
ta mallaki Gumel da farko, mulkin Borno bai taka kara ya karya
ba, domin masarautar Gumel ta balle daga 'kar'kashin Borno
ta yi tsayuwarta ta kanta a 1837.
Tarihin yake-yaken Gumel ya faro ne tun daga karni na goma
sha takwas, zamanin sarki Kalgo (1804-1811) wanda ya dinga
kare garin Gumel, daga hannun mayakan Kano da kuma Machina
har sai lokacinda wani bawan sarkin Machina ya sami fili ya
soke shi da makami ya masa raunin da ya karasa shi har lahira.
Saboda kwadayin samun fa'Da'Da 'Kasa, da 'Yancin kai, wanda
jama'ar Gumel suka fara nunawa tun fil azal, yasa sun kutsa
kai wanjen ya'Ke wanda ake kira da "karo daya tsakanin
kyai da dutse", suka fara yakar garuruwa wanda har ya
sa ratar mil tamanin ne kawai ya raba su da shiga cikin garin
Kano.
A wani fage da Gumel ta taimakawa Kano za a iya samun karin
haske irin kwazon jaruman Gumel a ya'ke-ya'ken da suka goyi
bayan kungiyar Yusuf a tsakaninsu da askarawan Tukur na yakin
(1893-1895).
Wata yar gajeruwar jawabi da Gwadabe ya zayyana, ta ambaci
irin kwarewa, jarunta, da kuma tsarin askarawan Mangawa, tun
lokacin da suka soma fa'Dace-fa'Dacen su a mazaunin su na
farko a Dogoma. A cikin wannan jawabin Gwadabe ya kwatanta
irin shirin Mangawa da na askarawan Shehun Borno, inda shi
shugaban askarawan ke bada umurni, kuma yake tafiyadda fasalin
hare-haren askarawan sa baki 'Daya. Da farko Shiga cikin mayakan
Mangawa an takaita shi tsakanin yan sarauta kawai, ko da shike
irin wannan daukar na saukaka samun maya'ka, yana kuma toshe
armashin samun kwararrun askarawa. Bisa wata yar tarzoma a
shekara ta 1852 Mai Muhammadu Cheri ya fa'da'da daukar askarawa,
ya bu'Da kofar dauka ga duk mai niyyar shiga, ya kuma sau'ka'ka
wa wasu kwararrun maya'ka ko da basu da jinin sarauta zasu
iya shiga kwamban askarawan.
A zamanin sarki Dan Auwa (1811-1828). Gumel ta yi nasara
a yake-yake da makwabtanta da dama. A wani farmaki da yakai
wa Hadejia, ya sami galabar kutsawa har yazuwa garin Kaugama,
da Turmi. Daganan ya hada kai da sarkin Kano Dabo wanda yin
hakan ya kasance masa alheri. A wani harin ba zato ba tsammani
da yakaiwa Ringim, saboda karfin kariya daga mayakan Ringim,
harin ya fi karfin Dan Auwa, sai ya janye maya'kansa suka
koma garin Matoya can wajejen arewa maso gabacin garin Sule
Tankarkar. Bayan wata yar gajeruwar hutu sai suka fusata suka
kutsa har saida suka kore mayakan Kano din domin irin lahani
da raunuka da suka ji musu. Bayan mutuwar Dan Auwa, ba a yi
wani babban ya'ki ba, sai dai wasu yan tashe-tashen hankali
da aka samu tsakanin Gumel da garuruwan Zinder da kuma Hadejia
da kuma Kano, wanda bayan sune hadejia a sheka ta 1872 ta
sami cin galaba kan mayakan Gumel din a Zaburam. A wannan
harin ne aka kasha Sarkin Gumel Abdullahi, abinda ya kawo
sanadin karshen ya'ke-ya'ke tsakanin Gumel da Hadejia wadda
ya'ki ci ya'ki cinyewa, har wajen misalin shekaru hamsin.
Banda haka kuma, Gumel ta sha wuya a hanun makwabtanta daga
arewa musamman ma daga hannun sarki Ibrahim na Damagaram.
Can daga baya dai ta wajejen 1872-1896 mayakan Damagaram din
suka dinga cin zalin mayakan Gumel din akai-akai wanda kuma
shine sanadin raguwan yawan al'uman Gumel. Bugu da kari kuma,
yayin da sarki Rabeh ya dinga matsawa Gumel shi ne ya sa sarki
Ahmadau na Gumel wanda ya yi sarauta tsakanin 1896-1915 ya
damu har ya je ya nemi mafaka da tsaro a hannun Lord Lugard
a 1903 wanda bayansa ne al'umarsa suka dinga dawowa gida domin
ci gaba da fatauci da kuma rayuwarsu cikin lumana.
|
|