|
Kamar yadda aka sani dai, ba kasafai kawai mutane ke tattare
kwan su da kwarkwatarsu su tasamma hanya haka kwatsam kawai
domin kwadayin balaguro ko kuwa kwadayin wata fadar ba. Akwai
dalilai masu dama da suka sa Mangawa na farko, yawan kaurace
kauracen nan. Irin dalilan sun hada da neman guri mafi amfanin
gona, guje ma fadace-fadace, yake-yake, rashin jituwa tsakanin
hakimai, da manyan gari da sarakuna. Bugu da kari, akwai kuma
wasu dalilai da suka hada da rashin jituwa da masu masauki,
watau famar matsantawa daga yake-yake da Mai (sarkin) Borno
wanda shine ya zama dalilin hijira da kuma hangen samun bunkasarshiyar
filin noma domin samun amfanin gona da kuma makamantansu.
Masana tarishi sun yi imani da cewar a wannan lokacinne aka
kirkiro, wannan gagarumar fadar ta Tumbi, wadda a cikinta
ne aka soma amfani da tsarin mulki, wadda kuwa, har yau, da
irinsa ake mulkin. Banda haka kuma, a wannan zamanin ne hukumar
Tumbi ta sami askarawan tsaro masu kwazon gaske, da har ta
zama abin alfahari. Wasu daga cikin gagararrun askarawan zamanin
wanda suka cancanci a ambacesu sun hada da danjuma na Farko,
Adamu Karro, Muhammadu mai kota, da dan Auwa, wadanda sune
suka jagoranci nasarar kwatan yancin kai daga hannun hukumomin
da ke mulki a kasar Borno.
Masu Magana dai sun ce, “taho mu zauna, shike zama taho mu
sa$a”. Tarihi kuma ya nuna cewa an sami rashin jituwa ainun
tsakanin wadannan fadodin guda biyu, musamman ma da yake haryau
ana zargin Mai (Sarki) Borno da laifin kashe daya daga cikin
jaruman Gumel, watau mai suna dan Auwa a Nguru a 1828, a yayinda
shi dan Auwan ya guji bada nasa toshin (kyautar sarki) da
aka sabunci baiwa masu sarauta.
Rashin bada wannan kyatar sarki da dan Auwa yaki, yasa Mai
(sarkin) Borno da Damagaram suka farmasu da hare-haren yaki
lokacin da suke Nguru, har kusan 1830-1840 wanda ya kawo sanadin
da masu garin Gumel suka ga cewa idan ba sun guje wa wannan
zangon ba, su da samun kwanciyar hankali zai yi wuya. Wannan
itace basirar tashinsu daga kusa da Borno suka yada zango
a garin da ya zame musu babban birni, watau garin Gumel, an
kafa garin Gumel a shekara ta 1845. Koda yake sabuwar birnin
fadar Gumel ta fada cikin zangon Sokoto ne, masarautar Gumel
basu bada hadin kai ga sarakunan Sokoto ba, sai suka ci gaba
da hada kansu da sarakonan Borno, har ya zuwan bayyan turawa
a yankin. A takaice dai watau su Mangawa mutane ne masu wata
shahararran tarihin kaurace-kaurace mai ban sha’awa, kuma
mai yawan al’ajibi.
Kafin Mangawa su yada zango a Gumel, yankin gandun daji ne
kawai, wanda bashi da iyaka, a lokacin banda filani masu kiwo
babu wani wanda ya ta$a tunanin kafa wane gari ko kuma wata
irin nuna sha’awar yin haka din a gandun dajin da yau ya zama
babban birnin larden Gumel na yanzu.
Masana labari sun hakikance sarkin garin Tumbi na takwas
watau Mai Muhammadu dan Tanoma na gidan Muhammadu Maikota
ne ya kafa garin Lautai watau Gumel. Hakika, kashe Dan Auwa
da kuma yawan halaka jama’a da dukiyar da aka tabka wa kasar
Gumel a zamanin da suka kara da Shehun Borno ya ciwa mutanen
Gumel tuwo a kwarya ainun, har ya kuma rage musu karfin shaharan
da aka san su da shi wajen yaki. Wannan ya gurguntar askarawan
Gumel baki daya. Ana kuma zaton cewa wannan shi yasa Sarkin
Damagum Sarki Ibrahim ya raina Gumel ya dinga kai musu hare-hare
akai-akai domin neman ya mallakesu baki daya.
Babu shakka wannan hare-haren da kuma wata sammaci da Shehu
Laminu ya masa a 1830 ne, suka sanyo dalilan gudon Muhammada
Mai dan Tanoma ya dinga yi har sai daya yada zango a garin
Gumel na yanzu a 1837.
Banda kuma irin hare-haren da aka yi ta kai wa Gumel, kwadayin
samun yancin kai daga karkashin hukumomin Damagun, da kuma
Borno, suna cikin dalilanda suka sa Mai Dan Tanoma ya nemi
shawarar wani bokansa wanda ake zaton cewa shi ne ya basu
sa’a ta kauracewarsu zuwa wannan garin na yanzu da ake kira
Gumel. Masana tarishi sun ambata a cikin tarihin Gumel cewa
shi wannan mai tabaron hangen nesan ( Malamin Sarki) ya zana
ayoyin al kur’ani ya baiwa wata saniya ta hadiya sa’annan
yace a dinga bin ta sai inda ta tsaya taye fitsaren wannan
rubutun sai su yada zango ya zame musu nasu sabon mazaune
(garin).
Tarishe ya sanaddamu cewa saniyarce ta kada ta yi yamma kuma
wasu shaharrarun mallamai kalilan suka dinga binta a baya,
wannan saniyar takan tsaya a kowane tabki kokuma gulbe tadan
sha ruwa ta ci gaba, sai da ta iso wannan jejin sai ta tsugunna
a unguwar zuwo tayi fitsaren rubutun, da ganin haka sai wanda
suke biye da ita suka ce Lau-ta-yi wanda ya sa aka rada wa
garin suna Lautayi da farko, kamin a sake sunan zuwa Gulbe,
wanda kuwa shine sunan saniyar. Ita kuma saniyar ta sami sunanta
ne daga irin halinta na shan ruwa daga kowane gulben da ta
samu a kan hanyarta a lokacin da ake biye da ita.
A wata siga dabam kuma da ke fadin cewa garin Gumel ya faru
ne a yayinda tafiye-tafiyen Mangawa a karkashin jagorancin
Muhammadu kanin Mai sarkin Ngazargamu, wanda shine sarki na
goma sha shidda. Wannan sigar kuwa tana fadin cewa an sami
rashin jituwa kan wata dukiya da ta shafi biyan kudin wani
doki wanda shi sarki Muhammadu ya guji hukuncin da ya kamata
a masa. Tare da jama’arsa baki daya, Muhammadu ya dauki dukiyarsa,
da iyalansa, dakuma kannuwansa guda biyu. Suka kama hanya
da manufar zuwa garin Ligalu a kasar Nijar, mai nisan kimanin
mil dare biyu daga Gumel. Kafin su sami dacacciyar mafaka.
Wannan kwambar kuwa sun yi ta tsaye-tsaye a garuruwa da dama
da suka hada da birnin Shadika, Babaye, da kuma Dogama inda
suka sami karin tarago har ma ya kai da cewa shi sarki Muhammadu
ya dauki matakin nada shugaba a cikinsu. Nan ne wani kanin
sarkin mai suna Adamu na Tsohon Birni ya sami daukaka, aka
nada shi sarki, wanda ya zamanto mukaminsa na tsawon shekaru
talatin (1719-1749), ko da shike muna iya tuna cewa Muhammadu
mai kota ne yayi sarauta daga 1777 zuwa 1804, a yayin da ya
zama sarkin farko da Mai Borno ya nada a yadda tarihi ya nuna.
Kuma dama shine ya yi sarautar Tumbi tun asali, wannan shiyasa
har kwanan gobe akwai zumunci da ma’amala tsakanin jama’ar
Tumbi da kuma mutanen Gumel.
Bugu da kari kuma, kafin nasara (Yan mulkin mallaka) su raba
iyaka tsakanin kasar Nijar da Nijeriya a watan june 1898,
duka gundumomin da ke kimanin mil ishirin daga garin Gumel,
na biyan diyarsu (haraji) ga masu sarautar Gumel a wancan
zamanin. Kazalika kuma, har ila yau, mazauna garuruwa da dama
a cikin Nijar wadanda suka hada da Maloua, Dingas, More da
Damagum suna ci gaba da ma’amala da jama’an Gumel, ta fannin
ziyarce-ziyarce a lokacin bukukuwa da kuma makamanninsu.
Tarihi dai ya nuna cewa Muhammadu Mai Tumbi, sarkin Gumel
na takwas, ne ya kafa garin Gumel domin irin kwazon da ya
nuna a lokacin da yake sarauta. Mai Tunbi yayi shekaru tara
a Tumbi kafin ya zo ya yi shidda a Gumel, a cikin garin Gumel
na yanzu ya rubuta wasikar murabus zuwa ga Shehun Borno a
shekarar ta 1843, inda ya ambaci cewa shi dai ya manyanta
kuma yana neman izini ya sauka daga karagar mulki. Nan ne
ya mika wa dansa, watau Cheri karagar mulki.
|
|