|
Tarihi ya nuna cewa Mangawa (Barebari) suka kafa Garin Lautai,
Wanda a zamanin yau ake kira Gumel. Kamar yadda Masana tarishi
suka bayyana cewa Mangawa (Barebari), sun kauro ne daga kogin
Maliya a kasar Masar, suka dinga yada zango a gurare daban-daban
har sai da suka sami yada wani gagarumin zango a Ngazargamu,
a kudancin Cadi. Wannan shine babban yada zango da suka yi
a shekara ta 1480, wanda shine lokacin da aka kafa ta karkashin
Shehun Borno, kamar yadda aka santa a yau. Bayan karamin lokaci
ba da jimawa ba, sai wadannan bakin suka sake kwasar kayansu
suka yi gaba. Wannan karon shine kuma suka doshi yamma saida
suka dangana da wata fada mai suna Tumbi, suka huta sa’annan
suka kara kutsawa zuwa Gumel, inda suka kafa masaukinsu na
karshe, tsakanin 1729-1848.
|
|
|
|
|
|
|
Masana'antu Da Tattalin Arzikin Gumel
|
Ma Shimman Gurare A Kasar Gumel
|
|
|